Wasu daga cikin kasashen Larabawan Afirka da suka hada da Aljeriya na kokarin ganin an kwace kujerar da aka bai wa Isra’ila a matsayin mamba mai sanya ido a kungiyar tarayyar Afirka.
Haka nan kuma ba ga wadannan kasashe akwai wasu daga cikin kasashen da ake sa ran za su goyi bayan wannan matsaya da wadannan kasashen suka dauka, daga cikin kasashen akwai Gabon, Senegal, Mali, Nijar, Najeriya, Tanzania, Afirka ta Kudu, Zimbabwe, Iretrea.
Tun kafin wannan lokacin wasu daga cikin wadannan kasashe sun nuna rashin gamsuwarsu da wannan mataki, musamman kasar Afirka ta kudu, wadda ta fito a hukuamnce ta yi Allawadai da hakan, tare da bayyana shi a matsayin halasta zaluncin Isra’ila a kan al’ummar Falastinu.
Kamar yadda ita ma gwamnatin Aljeriya ta bayyana cewa, an yanke hukuncin yin hakan ne kawai ta hanyar daukar ra’ayoyin wasu, amma ba ra’ayin dukkanin kasashe mambobi na kungiyar ba.
A kan haka Aljeriya ta ce ba za ta taba goyon bayan baiwa Isra’ila kujera a matsayin mamba ‘yar kallo a cikin kungiyar tarayyar Afirka ba, domin kuwa yin hakan ya yi hannun riga da manufofin siyasar kungiyar, wadanda suka ginu a kan kare hakkokin bil adama a duk inda suke a duniya.
Haramtacciyar kasar isra’ilan dai tana fuskantar kyama daga mafi yawancin kasashen duniya duba da yadda take take hakkin dan adam tare da kashe raunana falasdinawa gami da kwace musu gidajen su a yankin west bank da kuma sheikh jarrah da dai sauran bangarori na kasar falasdinu.
Firayi ministan haramtacciyar kasar yahudawan ta isara’ila dai a baya bayan nan ya nuna damuwar sa kan yadda ake nuna kyamar yadudawa musamman haramtacciyar kasar tasa ta isra’ila amma amsar daya samu daga kasashen duniya itace, kyamatar haramtacciyar kasar isra’ilan ta samo asali daga mummunan zaluncin da suke gudanarwa a kan raunanan falasdinawa wadanda basu ji ba basu gani ba.