Wannan kuwa na zuwa ne bayan da shugaban Faransa Eammanuel Macron ya cacaki wata jaridar kasar mai suna Le Monde da ta wallafa labarin cewa Faransar ta yi wa Algeria Mulkin mallaka cikin Zaluci abin da ya yi wa Algerian zafi.
Da take karin bayani kan janye jakadan, fadar shugaban kasar Algeria ta ce nan gaba kadan zata fitar da sanarwa wadda cikinta zata mayarwa da shugaban Faransan zazzafan martani.
Matakin na Algeria na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman tankiya tsakanin kasashen biyu, biyo bayan matakin Faransa na rage yawan bizar da take bai wa ‘yan Algeria, Morocco da Tunisia.
Awani labarin na daban kuma a wannan Lahadi 19 ga watan Satumbar 2021 akayi jana’izar Abdelaziz Bouteflika, tsohon shugaban kasar Algeria da ya fi dadewa a kan mulkin kasar da ke Arewacin Afirka, inda aka binne shi a makabartar gwarzayen ‘yanci amma ba tare da girmamawar da akayiwa magabatansa ba.
Tsohon sojan ya yi murabus daga mukaminsa a watan Afrilu na shekarar 2019 bayan da sojoji suka yi watsi da shi sakamakon makonni na zanga – zangar adawa da shirin sa na tazarce a karo na biyar.