Hedikwatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar da cewa tawagar Amurka ta je Yamai a makon jiya ne domin nuna damuwarta dangane da alakar da ke tsakanin Nijar da Rasha da Iran, ko da yake daga bisani Nijar ɗin ta yanke ƙawancen soji da ke tsakaninta da Amurka mai soji kusan dubu a ƙasar.
Pentagon ta ce a halin yanzu tana nazari kan batun mafita dangane da wannan lamarin.
A sanarwar da sojojin na Nijar suka fitar a ranar Asabar, sun ce sun yanke duk wata hulɗa da ta danganci haɗin-kai ta fannin soji da ƙasar Amurka “nan-take”.
Mai magana da yawun Pentagon Sabrina Singh ta ce “Tawagar Amurka ta je can ne domin nuna damuwa kan wasu lamura… Mun damu kan hanyar da Nijar ta ɗauka.”
Yauƙaƙa dangantaka da Rasha
Tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji aka yi a watan Yulin 2023, sojojin na Nijar suka ɗauki matakin fatattakar sojojin Faransa da na wasu ƙasashen Turai daga ƙasar tare da sanar da ficewarsu daga ECOWAS.
Kamar sauran sojojin da ke mulki a Mali da Burkina Faso, ita ma ƙasar ta ƙara yauƙaƙa dangantakarta da Rasha.
Wasu manyan jami’an gwamnatin Rasha daga ciki har da Yunus-bek Yevkurov, wanda shi ne mataimakin ministan tsaron Rasha sun kai ziyara Nijar inda suka haɗu da sojojin da ke mulkar ƙasar.
Firaiministan gwamnatin ta Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya kai ziyara Iran a watan Janairu.
‘Zargi maras tushe’
A sanarwar da suka fitar a ranar Asabar, sojojin na Nijar sun yi watsi da zargin da Amurka ta yi kan cewa Nijar ɗin “ta saka hannu kan yarjejeniya ta sirri da Iran game da ma’adinin Uranium.”
DUBA NAN: Sojojin Najeriya Sun Hallaka Babban Dan Ta’adda, Kachalla Damina
Sai dai Singh ba ta yi wani ƙarin haske ba dangane da batun zargin alaƙar Nijar ɗin da Iran.