Wasu fararen hula 7 na kasar Labanon sun yi shahada a birnin Nabatie da ke kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: fararen hula da dama ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon harin da jiragen yakin gwamnatin yahudawan sahyoniya suka kai kan wani gini da ke birnin Nabatie da ke kudancin kasar Labanon.
Kafafen yada labaran kasar Labanon sun rawaito cewa adadin shahidan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai wa wannan gidan nasu ya kai mutane 7, kuma dukkaninsu fararen hula ne, sabanin ikirarin sahyoniyawan babu wani soja a cikinsu.
Har ila yau a yammacin jiya Laraba jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a yankunan kudancin kasar Lebanon, da suka hada da kauyukan Adshit, Al-Shahabieh, Al-Swaneh, Al-Jobor Heights, da kuma yankin Al-Tafah.
Kuma jiya da yamma ne wani iyali farar hula da suka kunshi uwa da yara 2 suka yi shahada sakamakon harin bam da gwamnatin Sahayoniya ta kai a garin Al-Swaneh da ke kudancin kasar Labanon.

Source: ABNAHAUSA