Ta hanyar aika daidaikun wasiku zuwa ga shugabannin kiristoci na duniya da shugabannin jami’o’i na coci-coci, shugaban Jami’ar Al-Mustafa ta duniya ya taya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen Annabi Isa (AS) da kuma murnar fara sabuwar shekara, domin bayyana shirin hadin gwiwa da hulda tsakanin mabiya addinai daban-daban, musamman wajen kare wadanda ake zalunta a Gaza.
Ta hanyar aika daidaikun wasiku zuwa ga shugabannin kiristoci na duniya da shugabannin jami’o’i na coci-coci, shugaban Jami’ar Al-Mustafa ta duniya ya taya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen Annabi Isa (AS) da kuma murnar fara sabuwar shekara.
Domin bayyana shirin hadin gwiwa da hulda tsakanin mabiya addinai daban-daban, musamman wajen kare wadanda ake zalunta a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Dr. Abbasi, shugaban jami’ar Al-Mustafa Al-Alamiya, a cikin sakonsa na taya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa Almasihu mai albarka As taya murnar farkon shekara ta 2024 miladiyya, inda ya kawo wasu sassa na Littafi Mai Tsarki da kuma maganganun Amiral-Mu’uminin Ali A cikin Nahj al-Balaghah, ya kawo cewa bada kariya ga wanda ake zalunta na daya daga cikin mafi muhimmancin ayyuka na manyan mutane, shugabannin addini da masu ilimi kuma tushe ne na mutumtaka. Kuma ya kira masu dukkan masu tunani, da ‘yan siyasa don yakar zalunci da kisan kiyashi da gwamnatin sahyoniya take yi wa al’umma, azzaluman Gaza da su farka.
Shugaban jami’ar Al-Mustafa a sakonsa na sabuwar shekara ga Paparoma, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, shugaban majalisar tattaunawa kan addinai, shugaban majami’ar addini, shugabannin darikar Katolika na duniya. Romania, Jojiya da Rasha, Kiristanci na kasashen Larabawa na Masar, Labanon, Iraki da Gabashin Turai, da jakadu Shugabannin jami’o’i da ministocin kimiyya da al’adu na Venezuela, Brazil, Bolivia, Nicaragua, Cuba da Kenya ya sanar da su shirin Jami’ar Al-Mustafa Al-Alamiya a matsayin cibiyar ilimin jami’ah da Hauza ga duk wani hadin gwiwa da mu’amalar hulda tsakanin mabiya addinai, musamman a batun kare zaluncin da ake gudanarwa a Gaza.
Source: ABNAHAUSA