Rahotanni daga Isra’ila na cewa ƴan sanda da masu bincike sun kai samame ofisoshin Al-Jazeera da ke Birnin Ƙudus inda suka ƙwace kayayyakinsu na aiki.
Ministan sadarwa na Isra’ila Shlomo Karhi ne ya tabbatar da hakan jim kaɗan bayan gwamnatin Isra’ilar ta ɗauki matakin rufe ofisoshin na Al-Jazeera a faɗin ƙasar.
Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda jami’ai a cikin farin kaya suke kwance kyamarorin kafar watsa labaran a wani ɗakin otel wanda kafar ke amfani da shi a matsayin ƙwarya-ƙwaryan ofishi.
An samu “ci gaba” a tattaunawar da ke faruwa tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas kan tsagaita wuta a yaƙin Gaza, in ji kafofin watsa labaran Masar, sai dai sun yi gargaɗi cewa sai an yi taka-tsantsan.
“Wata majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa an samu ci gaba game da tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza,” a cewar kafar watsa labarai ta Al Qahera News.
Sai dai majiyar da ba ta so a ambaci sunanta ta ƙara da cewa: “Abubuwan da aka wallafa a kafofin watsa labarai game da yarjejeniyar ba gaskiya ba ne.”
Majiyar ta ce “wakilan jami’an tsaron Masar suna ci gaba da tuntuɓar dukkan ɓangarorin,” inda ta ƙara da cewa “dawo da Falasɗinawan da aka raba da gidajensu zuwa arewacin Gaza na cikin yarjejeniyar”.
Ana sa ran ci gaba da tattaunawa a Masar a ranar Lahadi kan batun tsagaita wuta a Gaza a yayin da Isra’ila ke matsa ƙaimi wurin luguden wuta a kan Falasɗinawa.
Ƙungiyar Hamas ta ce ta yi watsi da duk wata yarjejeniya da ba za ta kawo ƙarshen yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza ba sannan ta zargi firaiminista Benjamin Netanyahu da “yin ƙafar-ungulu” a yunƙurin cim ma yarjejeniyar.
Tun da farko, masu shiga tsakanin na Qatar, Masar da Amurka sun gana da wakilan Hamas a birnin Alƙahira kuma wani babban jami’i na Hamas da ke cikin tattaunawar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa za a gudanar da “sabon zagaye” na tattaunawa a ranar Lahadi.
DUBA NAN: Kwamitin Tuntuba Kan Gaza Ya Soma Zama
Masu shiga tsakanin, waɗanda suke nema Isra’ila ta daina kai hare-haren da ta kwashe watanni bakwai suna kai wa a Gaza, sun bayar da shawarar a tsagaita wuta ta kwanaki 40 tare da sakin Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su da kuma Falasɗinawan da ke ɗaure a gidajen yarin Isra’ila.