Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Rasha Al-Yum cewa,
a cikin wata sanarwa da cibiyar Azhar ta fitar ta bayyana cewa: Al-Azhar na girmama wannan jajirtaccen matsayi na Vladimir Putin wanda ya dauki kur’ani mai tsarki da kare al’amura masu tsarki na musulmi tare da nuna mutunta addinin musulunci.
A lokacin da yake karbar kwafin kur’ani a matsayin kyauta a birnin Darband na kasar Rasha, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi Allah wadai da matakin kona kur’ani mai tsarki tare da daukar wannan mu’amala da littafin musulmi a matsayin babban laifi.
A yayin ziyarar da ya kai a masallacin Juma’a na Darband, shugaban kasar Rasha ya bayyana cewa: “Jagoran kiristoci na Rasha a ko da yaushe yana tabbatar mana da cewa musulmi ‘yan uwanmu ne kuma duk abin da ya shafe su ya shafe mu ma.”
Ya kara da cewa: Hakan zai karfafa hadin kan al’ummarmu. Kasarmu kasa ce da ta kunshi bangarori daban-daban, amma al’umma daya ce. Wannan littafi mai tsarki ne ga musulmi kuma yana da tsarki da girma ga wasu ma wadanda ba musulmi ba.
Mun san cewa a wasu kasashe suna nuna hali daban, wasu kuma ba sa mutunta addinin mutane, suna cewa wannan ba laifi ba ne.
Ya ce: “Kona kur’ani a kasarmu ana daukarsa a matsayin bababn laifi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada a cikin sashe na 282 na kundin hukunta laifuka na kasar Rasha.
Wannan na zuwa a daidai lokacin da aka kona kur’ani mai tsarki a kasar Sweden tare da bayar da izinin yin hakan daga hukumomin kasar a matsayin ‘yancin bayyana ra’ayi.