Akallah sojojin Ivory Coast biyu da wani dan sanda guda suka mutu jiya Asabar lokacin da motarsu ta taka nakiya da aka binne a kan hanya a arewa maso gabashin kasar.
Majiyar tsaron kasar ta ce “fashewar ta kuma jikkata mutane uku .” Kuma hakan na zuwa mako guda bayan wani hari da wasu da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kashe wani sojan Ivory Coast a garin Tougbo ‘yan kilomita kadan daga kan iyaka da Burkina Faso.
Cibiyar horas da yaki da ta’addanci
Wannan harin na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da Ivory Coast da Faransa suka kaddamar da wata makarantar horon yaki da ta’addanci a kusa da Abidjan da nufin Akallah bunkasa karfin yankin Sahel na dakile barazanar jihadi da ke yaduwa.
Masana harkar tsaro sun yi gargadin cewa kazamin yakin jihadi na yankin na iya bazuwa kudu zuwa kasashen da ke gabar tekun Guinea.
Karuwar hare-hare
Wannan shi ne karo na hudu da aka kai hari a kasar Cote d’ivore dake yankin yammacin Afirka cikin sama da watanni biyu.
Rikicin na baya-bayan nan ya fara ne tun a watan Maris, lokacin da wasu suka kashe wasu jami’an tsaron Ivory Coast uku a wani tagwayen samame da suka kai a kan sansanin sojoji a kusa da kan iyaka da Burkina.
Akallah ana kiyasta wannan daga cikin matsalolin da suka addabi nahiyar afirka, musamman yadda kasashen ketare suka mamaye harkar tsaron kasashen afirka.
”Manyan kasashen turawa sun kakkame tsaron kasashen afirka kuma ana zargin sune suka samar yawaitar tashe tashen hankula a garuruwa” Inji wani mutum.