Wasu bayanai na daban sun ce bam ne ya tashi kuma akalla an samu mutane da dama da suka mutu wasu kuma sun jikkata.
Rahotanni sun ce mutum akalla 13 suka mutu a harin da suka hada da mata da yara.
Kafin hakan dama kasashen Amurka da Burtaniyar sun yi gargadi game da barazanar kai hari filin jirgin saman na Kabul, suna jan hankalin yan kasashensu da kada su yi balaguro kasar.
Wasu rahotanni suna cewa ana kyautata zaton cewa akalla akwai sojojin Amurka hudu a cikin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari.
An shawarci wadanda ke ciki a yanzu haka su tattara yanasu ya nasu su fice.
Gargadin na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Shugaba Biden ya yi karin haske kan hadarin da masu tsattsauran ra’ayi da ke da alaka da kungiyar ISIS ke haifarwa.
Rahotanni daga Kabul sun ce ‘yan Taliban sun rufe dukkan hanyoyin shiga filin jirgin saman.
Haka kuma Kasashe da dama sun gargadi ‘yan kasarsu da kada su filin jirgin saman saboda bararazanar dake akwai.