Yayin da kasashen duniya ke yi wa Rasha ca kan mamayar Ukraine, a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kuwa ‘yan kasar na jinjinawa sojojin hayar wani kamfanin samar da tsaron na Rashan da suka ce sun taimakawa kasar da yaki yadai-daita wajen maido da doka da oda.
A wani labarin kuma, an sako Sojojin Faransa hudu da ke aiki a karkashin Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadanda da ake zargi da yunkurin kashe shugaban kasar.
Sudai sojojin faransa an kama su dumumu da kokarin kisan shugaban kasan afirka ta tsakiyan wanda hakana ya sa aka tsare su na wani lokaci.
A wani labarin na daban kuma Novak Djokovic zai rasa matsayin na lamba day ana duniya a wasan kwallon tennis bayan da ya sha kashi 6-4 7-6 (7-4) a hannun Jiri Vesely, a wasan daf da kusa da karshe na gasar Dubai Championships.
A ranar Litinin mai zuwa, za a maye gurbin dan kasar Serbia din da Daniil Medvedev a matsayin lamba daya na wasan kwallon Tennis na duniya.
Vesely, dan kasar Jamhuriyar Czech wanda shine lamba na 123 a duniya a wasann Tennis, ya bayyana mamakinsa da nasarar da ya samu a kan lamba daya na duniya.
Medvedev, dan kasar Rasha, zai kasance dan wasa na farko, wanda ba Djokovic, Roger Federer, Rafael Nadal ko Andy Murray ba da ya haye zuwa wannan matsayi a cikin shekaru 18.