Afganiyawa Sun La’anci Amurka Kan Kwace Kudaden Kasar.
A Afganistan dubban jama’ar kasar ne suka gudanar da zanga-zangar adawa da matakin da shugaban Amurka Joe Biden ya dauka na kwace ajiyar kudaden kasar.
Masu zanga zanagr a lardin Bamyan a tsakiyar kasar, sun yi ta rera kalamai na nuna kyama ga Amurka.
A farkon wanan wata ne Biden ya sanya hannu kan wata doka, wanda ya ba da damar raba dala biliyan 7 na kadarorin da aka rike daga babban bankin Afganistan ga wadanda harin na 11 ga Satumba ya risa dasu.
Saidai ta ce za ta bayar da rabin a matsayin tallafi ga al’ummar ta Afganistan amma ga hannun gwammnatin Taliban ba.
Amurka ta rike kudaden ne, biyo bayan da kungiyar Taliban ta kwace mulki daga hannun gwamnatin Kabul a watan Agustan da ya gabata.
Kusan mutane miliyan 24 a Afghanistan kwatamcin kashi 60% na al’ummar kasar suna fama da matsananciyar yunwa, yayin da miliyoyi suka rigaya suka yi gudun hijira.