Afganistan; Taliban Tace Gazawar Gwamnatin Kasar Ba Abin Fata Ne Ga Kowa Ba.
Wani jami’in gwamnatin Taliban ta kasar Afganistan ya bayyana cewa gazawar gwamnatin kasar ba abin fata ne ga kowa ba.
Tashar talabijin ta kasar Cana CGTN ta nakalto Abdul Qahar Baikhi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Afganistan yana fadar haka a jiya Asabra, ya kuma kara da cewa, lokaci yayi wanda kasashen duniya zasu amincewa gwamnatin Taliban gudanar da harkokin kasar kamar yadda ko wace kasa take da wannan ‘encin a duniya.
Balkhi ya kara da cewa yanzu kimani shekaru 43 kasar Afagansitan tana cikin takunkuman kasashen duniya, wanda ya jefa mutanen kasar cikin wahalhalu da dama.
A cikin watan Augustan shekara ta 2021 ne kungiyar Taliban ta sake komawa kan madafun iko a kasar ta Afganistan bayan da Amurka ta fidda sojojinta cikin yamutsi da kuma gaggawa.
Taliban ta kafa gwamnatin rikon kwarya a cikin watan satumban da ya gabata, amma rashin kudi sanadiyyar takunkuman kasashen waje a kan kasar ya hanata dai-dai kasar, tunda a halin yanzu hatta wasu ma’aikatan gwamnati basa karban albashinsu saboda karancin kudade a bankunan kasar.
Babu gwamnatin wata kasa ko guda wacce ta amince da gwamnatin Taliban ta kasar Afganistan.