Adadin mutane da annobar korona ta kasha a kasae Brazil ya zarce dubu 600 don daga bullarta zuwa yammacin Jumma’a.
Ita ce kasa ta biyu mafi muni a duniya a yawan adadin mutanen da cutar ta kashe bayan Amurka, kodayake masana da dama na da shakku kan bayanan gwamnati dangane da wannan cuta.
A wani labarin na daban adadin mutanen da cutar Covid-19 ta harba a sassan Duniya yanzu haka ya zarce miliyan 100, yayında sama da miliyan 2 da dubu 100 saka rasa rayukan su.
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana aniyar sayen karin maganin rigakafi miliyan 200 domin amfani da miliyan 300 wajen yiwa jama’ar kasar rigakafi, a daidai lokacin da yake bayyana halin da Amurka ta samu kań ta a matsayin yanayin yaki.
A bangare guda Birtaniya ta zama kasa ta farko a Turai da adadin mutanenta wadanda Covid-19 ta hallaka ya haura dubu 100 inda Firaminista Boris Johnson ke cewa lallai nauyi ne daya rataya a wuyansu bayar da kariya ga rayukan al’umma kuma ci gaba da rasa rayukan mutanen sanadiyyar cutar na taba zuciyarsu matuka.
Tuni dai kasashen Duniya suka fara sake daukar tsauraran matakan dakile cutar ta hanyar kulle jama’arsu ciki kuwa har da Brazil a kan gaba kana Afrika ta kudu dai dai lokacin da kwararru ke bayar da shawarar daukar makamancin matakin a Faransa.