Adadin mutane da annobar korona ta kashe a kasar Amurka ya zarce dubu mutane dunu 700 tun bayan barkewar cutar zuwa ranar Juma’a.
Wannan na zuwa ne yayin da adadin wadanda cutar ke kashewa kulla yaumin ke kaiwa sama da dubu 1, a kasar da kashi 55.7 da al’ummarta Wannan na zuwa ne yayin da adadin wadanda cutar ke kashewa kulla yaumin ke kaiwa sama da dubu 1, a kasar da kashi 55.7 da al’ummartasuka karbi allurar rigakafin cutar.
Korona na ƙara yaɗuwa a Amurka musamman sabon nau’in Delta, inda lamarin ya fi kamari a jihohin kudancin kasar.
A wani labarin na daban shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa har yanzu China na rike da “mahimman bayanai” kan asalin annobar korona, yayin da hukumar leken asirin Amurka ta yi imanin cewa kwayar cutar ba wani makami bane da aka samar, sai dai akwai rarrabuwar kawuna kan ko ta bazu ne bisa kuskure daga dakin binciken kimiyya.
Shugaba Biden cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Jumma’a ya ce lallai “Akwai muhimman bayanai da China ta boye game da asalin wannan cuta, sakamakon yadda tun farko mahukunta a Beijin suka yi kokarin hana masu binciken kasa da kasa da jami’an hukumomin lafiyar shiga kasar.”
Tuni Ofishin jakadancin China da ke Washington ya musanta batun da ya alakata da siyasa.
Shugaban na Amurka ya kara da cewa, “Har ya zuwa wannan lokaci Chin na ci gaba da watsi da kiraye -kirayen tabbatar da gaskiya game da annobar, adai lokacin da sabbin nau’ukanta ke barazana da kashe al’ummar duniya.
Sanarwar na zuwa ne yayin da hukumar leken asirin Amurka ta gaza warware wata muhawara mai zafi tsakanin jami’an gwamnatin Biden kan ko cutar ta samo asaline daga dakin gwaje-gwaje kimiyar kasar China.