Adrian Zenz mamba a babbar cibiyar bin diddigin lamarin mutanen da tsarin gurguzu na kasar China ya ga bayan su da wadanda ake gallaza musu wato cibiyar (Victims of Communism Memorial Foundation) ya bayyana cewa, bisa binciken da aka gudanar, adadin ‘yan kabilar Uighur marasa rinjayea China zai raguda mutane miliyan 2.5 zuwa miliyan 4.5 daga nan zuwa shkara ta 2040.
Wannan kuwa zai kasance ne sakamakon yadda ake hana wadannan mutane haihuwa, har ana yi musu ukuba kan hakan, tare da kafa musu tsauraran dokoki na hana su haihuwa, wanda hakan ke nuni da cewa adadinsu zai ci gaba da raguwa kenan.
A wani labarin na daban kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na farko da ya gudanar a yammacin jiya Talata a birnin Kabul, bayan da mayakan kungiyar ta Taliban suka kwace iko da birnin baki daya.
Kakakin na Taliban ya ce ba su da makiyi a cikin kasar Afghanistan, hatta wadanda suka yi yaki da su, a halin yanzu gaba ta zo karshe, dole ne kowa da kowa ya zo a hada karfi da karfe domin gina kasa.
Haka nan kuma ya bayyana cewa, sun samu nasarar korar ‘yan mamaya daga kasarsu bayan kwashe tsawon shekaru ana mamaye da kasar, wanda a cewarsa hakan kokarin na dukkanin al’ummar kasar ba kungiyar Taliban kawai ba.
Dangane da ofisoshin kasashen ketare da ke kasar Afghanistan, Zabihullah ya bayyana cewa, za su kare dukkanin ofisoshin jakadanci na dukkanin kasashen ketare da suke a cikin kasar Afghanistan, tare da bayar da kariya ga jami’an diflomasiyya da sauran ‘yan kasashen waje da suke gudanar da ayyukansu a cikin kasar.
Ya ce za su baiwa al’ummar Afghanistan ‘yancinsu ba tare da tauye wa kowa hakkoinsa a matsayinsa na dan kasa ba, kamar yadda kuma za a kafa gwamnati wadda za ta kunshi dukkanin bangarori na al’ummar kasar baki daya, ba tare da mayar da wani bangare saniyar ware ba.