Abul Gaid; Iraqi Ta Tsallaka Hatsarin Fitina Da Ta Tunkareta.
Kungiyar kasashen larabawa ta yada da yadda ‘yan siyasa a kasar Iraqi suka iya tsallaka fitina da ta tunkari kasar a cikin makonnin da suka gabata bayan da magoya bayan gamayyar jam’iyyun Sadar suka mamaye yankin Green Zone na birnin Bagdad.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Ahmed Abulgaid babban sakataren kungiyar kasahen larabawa yana fadar haka a birnin Alkahira inda cibiyar kungiyar take.
Babban sakataren ya kara da cewa mutanen kasar Iraqi sun sha wahalhalu da dama, kowa yana son ganin kasar ta sami nutsuwa a bangaren siyasa tattalin arziki da kuma tsaron kasar.
READ MORE : Iran Tana Bukata Tabbatar Abubuwa 4 Kafin A Farfado Da JCPOA.
A cikin watan Octoban shekarar da ta gabata ce aka gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Iraqi amma har yanzun an kasa kafa gwamnati a kasar saboda sabanin siyasa a tsakanin yan siyasar kasar.
READ MORE : Iran Ta Rubutawa Kasashen Da Suke Daukar Bakwancin Sojojin Amurka A Yankin Wasikar Gargadi.
READ MORE : Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Zai Tattauna Da Kasar Qatar Kan Matsalar Makamashi.
READ MORE : Rashin Tsaro Da Zaman Lafiya A Kasar Yamen Na Shafar Yankin Yammacin Asiya Da Tekun Fasha Kai Tsaye.