Roman Abramovich ya yi tayin sayen Valencia da zarar an kammala sayar da kungiyarsa ta Chelsea.
Rahoton tayin sayen kungiyar Valencia da ke gasar LaLiga da attajirin na kasar Rasha ke shirin yi, ya zo ne bayan da aka alakanta shi da yunkurin sayen kungiyar Goztepe da ke gasar kwallon kafa ta kasar Turkiya.
A makon da ya gabata, wasu rahotanni suka ce Roman Abramovich ya shiga mawuyacin hali tun bayan da gwamnatin Birtaniya ta kwace kadarorinsa a makwannin baya, sakamakon mamaye Ukraine da kasarsa Rashan ta yi.
Attajirin kasar Rasha Roman Abramovich, ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar sayar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, shekaru 19 bayan mallakarta.
Attajirin ya kuma yi alkawarin bayar da gudummawar kudi daga cinikin saida kungiyar ta Chelsea da za a yi domin taimakawa wadanda yakin Ukraine ya shafa.
Abramovich mai shekaru 55 da haihuwa ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, sayar Chelsea shi ne mataki mafi dacewa da zai amfani kungiyar mai rike da kofin gasar zakarun Turai.
Wannan kuwa nada nasaba da mamayar da Rasha ta yi Ukraine, yayin da ake kallon Abramovich a matsayin daya daga cikin na hannun daman shuganan Rasha Vladimir Putin.
A wani labarin na daban Attajirin na Rasha ya kara da cewar, ba zai nemi kungiyar ta biya shi bashin da ya bata na fam biliyan 1.5 kwatankwacin dala biliyan 2.
Tun daga karshen makon jiya ne dai makomar Roman Abramovich a matsayin mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ke cikin barazana bayan wani attajirin Swizerland ya yi ikirarin cewa, tuni aka yi masa tayin sayen kungiyar ta Chelsea.
Biloniyan attaijirin mai suna Hansjorg Wyss ya shaida wa Jaridar Blick cewa, Abramovich na son raba gari da Chelsea cikin gaggawa bayan yin barazanar lafta masa jerin takunkumai a majalisar dokokin Ingila.
Tuni ma dai Abramovich din ya mika ragamar kungiyar ta Chelsea ga wasu mambobin kwamitin amintattu na kungiyar domin ci gaba da kula da ita.