Abin da ya sa na janye daga takarar shugaban kasa bayan an tara min kuɗaɗe – Adamu Garba.
Mutum mafi ƙarancin shekaru da ya nemi takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar APC mai mulki, ya sanar da janyewarsa.
Adamu Garba, ɗan shekara 40 ya yi zargin cewa sayar da fom ɗin takarar naira miliyan 100 da jam’iyyar APC ta yi ga masu neman takarar shugaban kasa mayar da siyasa kasuwanci ne.
Ya ce bisa la’akari da yadda aka taho da tsarin abubuwan baki daya, an mayar da neman takara kamar harkar kasuwanci saboda mutane basa kula da kwazon mutum da irin tsare-tsaren da mutum ke da su da zai kawo ci gaba a kasa.
Adamu Garba,ya ce,” Kamar an shuka rashin gaskiya ne a tsarin sayar da fom baki daya.2
Ya ce, a duk duniya babu inda ake biyan kudin siyan fom mai yawa kamar Najeriya.
“A don haka ni a matsayina na matashi ba zan amince da irin wannan tsarin siya na kudi ba, saboda hakan ya nuna wanda ba shi da shi ba zai yi takara ba,” in ji shi.
Ya ce, batun tara mini kudi kuma na nemi a tara mini su ne da amincewar ‘yan Najeriya, sannan an tara mini kudin ne saboda ana ganin zan iya yin abin da ya dace idan na samu mulki.
“To daga baya kuma da muka zauna muka tattauna sai muka ga cewa idan mun dauki kudi mun sayi fom din takara kamar mun bawa jam’iyya kudi ne don ba bamu takarar za a yi ba.
Adamu Garba, ya ce game da kudin da aka tara masa yanzu ya ce duk wanda ke son kudinsa to ya sanar zai turawa mutum kudinsa.
Wannan ne dai karo na biyu da ya nemi takarar shugaban ƙasa bayan yunƙurinsa na 2019, ba tare da ya sayi fom ba.