Abin da Malami ya ce kan goge sashe na 84(12) na dokar zaɓe.
Ma`aikatar shari`a a Najeriya ta ce za ta bi umurnin da wata babbar kotu ta bai wa ministan shari`a cewa ya goge sashe na 84(12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa gyara.
Sashen ya buƙaci masu rike da mukaman gwamnati su sauka daga mukamansu tun ana saura wata shida a yi zabe.
A ranar Juma’a ne Mai shari’a Evelyn Anyadiketa yanke wannan hukuncin inda ta ce wannan tanadin bai dace da kundin tsarin mulkin ba.
READ MORE : A Kalla Mutane 21 Ne Su Ka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Wani Harin Taáddanci A Nijar.
Ma’aikatar shari’a ta ce za ta yi aiki da hukuncin, kuma za ta tabbatar da an cire sashen, kamar yadda Mai taimaka wa Ministan shari’a kan hulda da jama`a Dr Umar Jibrilu Gwandu ya shaida wa BBC.
Ku saurari hirar Ibrahim Isa da Dr Umar Jibrilu Gwandu …