Yau Litinin ake bude taron shekara-shekara da ke hada shugabannin kamfanoni da masu masana’antu daga sassa daban – daban na nihiyar Afirka a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire.Taron wanda ake kira ‘’Africa CEO Forum’’, shi ne mafi girma da ke hada shugabannin kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a lamurran siyasa ta tattalin arziki a Afirka.
Taron na bana dai na samun halartar shugabannin kamfanoni da masana’atu sama da 800 daga kasashe 70 mafi yawansu na Afirka sai kuma wasu daga sauran sassa na duniya.
Shugabannin kasashe
Bayan ga ‘yan kasuwa daga fannoni daban daban, taron na yini biyu kamar dai yadda jadawalinsa ke nunawa, zai kuma samu halartar shugabannin kasashe da na gwamnatoci da dama daga Afirka, da suka hada da shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara mai masaukin baki, Macky Sall na Senegal da ke matsayin shugaban Tarayyar Afirka da kuma shugaban Ghana Nana-Akuffo Ado da ke rike shugabancin kungiyar Ecowas.
Bazoum da Osibanjo
Sauran muhimman bakin da ake dako a wannan taro na Abidjan da ke da manufar habaka kasuwanci da saka jari a Afirka, sun hada da Mohamed Bazoum shugaban Jamhuriyar Nijar da kuma mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.
An dai gayyato masana da dama ta fannin tattalin arziki musamman daga Bankin Duniya, Bankin Raya Kasashen Afirka da sauran cibiyoyi na kudade, don gabatar da jawabai da ke fayyace irin damarmakin da ke da akwai wajen gudanar da kasuwanci cikin sauki sauki a nahiyar, tare da yin tsokaci dangane da irin kalubalen da ake fuskanta sakamakon matsalaloli na yau da kullum da ke faruwa a duniya.