A ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta da kuma goyon bayan gwagwarmayar Palasdinawa a zirin Gaza, muna tabbatar da cewa tsare jirgin ruwan Isra’ila mataki ne na zahiri da ke tabbatar da muhimmancin da gasken sojojin Yaman… Abdul Salam.
Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na shafin sadarwar yanar gizo na Ahlul-Baiti (AS) ya habarta cewa, mai magana da yawun kungiyar Ansar Allah Muhammad Abdul Salam ya tabbatar da cewa, tsare jirgin ruwan Isra’ila wani mataki ne na zahiri da ke tabbatar da muhimmancin yi dagasken sojojin kasar Yemen wajen shirinta na shiga yakin teku, ba tare da la’akari da farashinsa da abinda zai jawo ba.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yammacin yau Lahadi, a dandalin (X), Abdul Salam ya ce: “A ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta da kuma goyon bayan gwagwarmayar Palasdinawa a zirin Gaza, muna tabbatar da cewa tsare jirgin ruwan Isra’ila mataki ne na zahiri da ke tabbatar da muhimmancin da gasken sojojin Yaman wajen yakin teku, ba tare da la’akari da farashinsa da abinda zai jawo ba” .
Ya jaddada cewa, duk wata nuna damuwa don hana faɗaɗa rikici ita ce ta a dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza, yana mai nuni da cewa aikin na yau shi ne mafari.
Ya kara da cewa: Dole ne duniya ta gane cewa laifuffukan da makiya Isra’ila suke aikatawa a Gaza sun wuce kowane iyaka da kuma keta kowane abu mai tsarki.
Kakakin Ansar Allah ya yi nuni da cewa: Wajibi ne ga duk wani mai ‘yanci a wannan duniya ya yi duk abin da zai iya don dakatar da kai hare-haren Isra’ila kan Gaza, yana mai jaddada cewa kalamai na kin jini da tofin Allah tsine ba su da wani amfani a cikin duniyar da kawai ba ta fahimtar komai sai yaren karfi.
Da yammacin jiya ne rundunar sojin Yaman ta sanar da kwace wani jirgin ruwan Isra’ila a wani farmakin da sojojin ruwa suka kai a tekun Bahar Maliya, tare da kai shi gabar tekun Yemen.
Source: ABNAHAUSA