Abdollahian Matakin Amurka Na Dage Takunkumi, Yana Da Kyau Saidai Bai Isa Ba.
Iran ta bayyana matakin Amurka na janye mata takunkumi kan ayyukanta na nukiliya na zaman lafiya, mataki ne mai kyau saidai bai isa ba.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ne, ya bayyana hakan yau Asabar sa’o’I kadan bayan da Amurka ta sanar da dagewa Iran takunkumin.
Matakin na Amurka dai ya zo ne a daidai lokacin da tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma a shekarar 2015 tsakanin Tehran da manyan kasashen duniya kan shirinta na nukiliya ta kai wani mataki na ci gaba, inda batun sassauta takunkumin ya zama babban batu.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka a ranar Juma’a ta ce ta dau wannan matakin ne domin taimakawa tattaunawar da ake.
Matakin a cewar labarin zai bai wa sauran kasashe da kamfanoni damar shiga shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya ba tare da sanya takunkumin Amurka a kansu ba, da sunan inganta tsaro da hana yaduwar makaman nukiliya.
A nasa bangare kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, ya ce matakin ba zai wani tasiri ba wajen farfado da tattalin arzikin kasar.
A shekarar 2018 ne tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar tare da sake sanyawa Iran takunkumin karya tattalin arziki, lamarin da ya sa jamhuriyar Musulunci ta fara aiki da wasu alkawuran da ta dauka karkashin yarjejeniyar.