Abdollahian; Isra’ila Ce Ummul Haba’isin Dukkanin Matsaloli A Gabas Ta Tsakiya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya bayyana a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Emirateriya cewa, muna son ganin kyautatar tsaro da ci gaba na makwabtanmu, amma yahudawan sahyoniya ne tushen rashin tsaro a yankin.
Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian da takwaransa na kasar UAE Abdullah bin Zayed Al Nahyan sun gudanar da tattaunawa ta wayar tarho domin tattauna halin da ake cikia yankin.
Ministocin harkokin wajen kasashen na Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da kuma na yankin da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa, da suka hada da halin da ake ciki a kasar Syria, Falastinu da kuma tattaunawar Vienna.
Shi ma ministan harkokin wajen Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, ya mika sakon taya murna shiga watan azumin Ramadan, wanda ya bayyana fatansa na ganin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da fadada a dukkanin bangarori.
Ya ci gaba da cewa, cin moriyar bai daya ta kasashen biyu ta dogara ne kan raya dangantakar dake tsakaninsu a fannoni daban daban, da lalubo hanyoyi na yin ayyukan hadin gwiwa.
Dangane da halin da ake ciki a yankin kuwa, ministan harkokin wajen hadaddiyar daular Larabawa ya bayyana cewa, a ‘yan makonnin da suka gabata al’amura sun inganta a yankin, kuma ziyarar da shugaba Bashar al-Assad ya kai UAE da kuma daukar matakin tsagaita bude wuta na wucin gadi a kasar Yemen, ya ba da dama ga kowa da kowa, domin ganin an inganta zaman lafiya da karfafa juna.