Abdollahian; Iran Ba Za Ta Yi Kasa A Gwiwa Wajen Kare Hakkokinta Ba.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya gargadi Amurka kan amfani da kalmomi na barazana a kan kasarsa da al’ummarta.
Amir-Abdollahian ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yammacin jiya Asabar a matsayin martani ga zargin da Amurka ta yi wa Iran a baya-bayan nan game da yunkurin kashe tsohon shugaban kasar Donald Trump da mataimakinsa kan harkokin tsaro John Bolton.
Ya kara da cewa, “Kokarin karkatar da hankulan al’ummomin duniya kan barnar da Amurka ta faka na kisan dubban daruruwan fararen hula a duniya, musammana yankin gabas ta tsakiya, ba zai yi amfani ba.
Ya ci gaba da cewa, Amurka tafi kowa sanin su wane ne suka kirkiro wannan magana da kuma manufar hakan a daidai wannan lokaci, saboda haka ta iya bakinta kan kalmomin da jami’anta suke furtawa a kan wannan lamari.
A ranar Laraba da ta gabata ce Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta tuhumi wani mutum mai suna Shahram Poursafi dan kasar Iran da kokarin shirya kisan Bolton a matsayin ramuwar gayya kan harin da Amurka ta kai a watan Janairun 2020 da ya yi sanadin shahadar Janar Qasem Soleimani.