Abdollahian; Bangarorin Vienna sun Kusa Cimma Yarjejeniya Kan Shirin Iran.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya ce an kusa cimma yarjejeniyar karshe tsakanin Iran da bangaren P4+1 a tattaunawar da ke gudana a tsakaninsu a Vienna kan farfado da yarjejeniyar shekarar 2015, amma akwai wasu muhimman batutuwa da ya kamata a warware su kafin nan.
Amir-Abdollahian ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi kai tsaye ta gidan talbijin a ranar Asabar ‘yan sa’o’i kadan kafin ziyarar da mataimakin jami’in kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Enrique Mora zai kai birnin Tehran, wanda kuma shi ne mai kula da shawarwarin da za a yi tsakanin Iran da sauran bangarori biyar da suka rage a tattaunawar.
Ya kara da cewa duk wata yarjejeniya da za a yi “ba za ta wuce tsarin JCPOA ba”, yana mai jaddada cewa, “Mun yi nasarar samun babban ci gaba a kan batun cire wa Iran takunkumi.”
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya kara da cewa, Mora zai isa Tehran nan da ‘yan sa’o’i kadan don tattaunawa kan sabon ci gaban da aka samu a tattaunawar Vienna.
Sannan kuma ya yi watsi da wasu rahotannin da kafafen yada labaran yammacin duniya ke bayarwa, da ke cewa Rasha ta yi garkuwa da yarjejeniyar karshe a Vienna sakamakon rikicin da ake fama da shi a Ukraine, yana mai cewa komai yana tafiya kamar yadda ya kamata.
Amir-Abdollahian ya ce Amurkawa sun nemi tattaunawa ta kai tsaye da Iran don tabbatar da abin da suka kira kyakykyawar niyya ta gwamnatin Joe Biden, ya ce amma Iran wannan ba shi ne muhimmi a wurinta ba, muhimmi shi ne Amurka ta aiwatar da abin da ya rataya a kanta.