A Yau Ce Kasar Iran Take Tunawa Da Kafa Dokar Maida Kamfanin Man Fetur Na Kasar Ya Zama Na Kasa.
Shekaru 71 da suka gabata ne wato a ranar 20 ga watan Maris na shekara ta 1951 aka kafa dokar maida kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar Iran ya zama na kasa, a lokacin shugabancin firai minister Dr Muhammad Musaddik.
Kafin haka kamfanin man fetur na kasar Burtaniya BP ne yake haka da kuma sarrafa danyen man fetur na kasar Iran.
Yau shekaru 71 da kafa wannan dokar, kuma a lokacin Musaddi ya sami wannan nasarar manya manyan kasashen duniya a lokacin sun kokarin ganin wannan dokar bata kai labara ba daga cikin sun kai kasar Iran Kotun duniya, amma sai ta sami nasara a kansu a shari’ar daga kasashen hukumar CIA ta Amuraka da wasu tokororinsu na kasashen yamma sun jagoranci wani juyin mulki wanda ya kifar da gwamnatin Dr Musaddik sannan suka dora wanda suke so kan kujerar Firai ministan kasar, wanda yasa dukkan kamfanonin kasashen yamma suka dawo Iran suna aikin har man fetur duk da cewa dokar tana nan.
READ MORE : An samu raguwar yawan man da Saudiyya ke hakowa bayan farmakin da sojojin Yamen suka kai.
Sai kuma bayan juyin jiya halin musulunci a kasar A shekara ta 1979 gwamnatin JMI ta katse hannun dukkan kamfanonin kasashen waje daga arzikin man fetur da gas na kasar Iran. Sannan cikin shekaru 43 da nasarar juyin juyha halain a halin yanzu kasar Iran tana samar da kasha 85% na kayakin da take bukata na haka da kuma sarrafa man fetur da gas da dangoginsu daga cikin gida.