Ma’aikatar lafiya ta Masar ta sanar a ranar Asabar din nan cewa a wani hatsarin jirgin kasa a kasar Masar mutum 49 sukn jikkata.
Ma’aikatar lafiya ta Masar ta sanar a ranar Asabar din nan cewa akalla mutane uku ne suka mutu wasu kuma suka jikkata sakamakon wani karo da wasu jiragen kasa guda biyu na fasinja suka yi a garin Zagazig da ke arewa maso gabashin birnin Alkahira.
Ma’aikatar ta kara da cewa biyar daga cikin wadanda suka jikkata na cikin rashin kwanciyar hankali.
An kai wadanda suka jikkata zuwa asibitoci kuma “ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto,” in ji ma’aikatar.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce daya daga cikin jiragen na kan hanyarsa ne daga Zagazig zuwa Ismailia, yayin da daya ke kan hanyarsa daga birnin Mansoura zuwa Zagazig.
Masar ta kwashe shekaru tana aiki don haɓaka hanyar sufuri ta tsufa, sabunta jiragen ƙasa, da haɓaka layin dogo.