A gurfanar da Taliban gaban kotu kan keta hakkin mata – Gordon Brown
Tsohon firaministan Birtaniya Gordon Brown ya shaida wa BBC cewa, yadda kungiyar Taliban ke ‘muzguna’ wa mata da ‘yan mata a Afghaninstan ”laifi ne na take hakkin bil-adama.
Mista Brown ya yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka da kasa-da-kasa (ICC) da ta gurfanar da shugabannin kungiyar a gabanta kan laifukan cin zarafin bil-adama.
Tun bayan kwace mulkin Afghanistan a shekarar 2021 Taliban ke ci gaba da kange mata da ‘yan mata daga gudanar da wasu abubuwa ciki har da zuwa makaranta da aikin gwamnati.
“Wannan babban cin zarafi da take hakkin mata da ‘yan mata ne,”in ji shi.
Yayin da yake zantawa da BBC, Mista Brown – wanda a yanzu ke zama jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan ilimi – ya ce a yanzu an kange mata daga samun ilimi, an toge su daga aikin gwamnatin, an hana su zuwa wurare da dama”
”Duk wannan nau’i ne na nuna bambanci tsakanin jinsi, kuma wannan shi ne mafi kololuwa a laifin take hakkin bil-adama da aka aikata a fadin duniya”, in ji shi.
Ya ce wasu na bayyana matakin da ‘wariyar jinsi’, kuma ”dole a dauki batun a matsayin cin zarafin bil-adama”, in ji Mista Brown.
“Dan haka hakki ne na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, wadda ke da alhakin daukar mataki kan laifukan da suka danganci take hakkin bil-adama, da bincike tare don gurfanar da masu laifi a gabanta”, in ji tsohon firaministan Birtaniyan.
Tsohon firaministan na Birtaniya – wanda ya jagoranci kasar daga shekarar 2007 zuwa 2010, na ganin matsin lamba kan gurfanar da kungiyar ka iya tilasta wa Taliban sake nazari kan matakan da ta dauka kan mata.
Mista Brown ya kuma yi kira ga gwamnatin Birtaniya da ta sanya wa shugabannin Taliban karin takunkumai, da shugabanni da malamai a kasashen musulmi domin jan hankalin ga shugabanin kungiyar.
Yana mai cewa addinin musulunci ”addini ne da ke mutunta mata ‘yan mata”.
Kalaman Mista Brown na zuwa ne a yayin da ake dab da cika shekara biyu da Taliban ta kwace mulkin kasar bayan kifar da gwamnatin dimokradiyya, bayan dakarun kasashen yamma sun fice daga kasar.
A lokacin da ta karbi mulki a 2021, kungiyar ta alkawarta amfani da dokoki masu sassaucia maimakon masu tsauri da ta yi amfani da su a lokacin ta ta yi mulkin kasar tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001.
A watan da ya gabata matan Afghaninstan suka gudanra da wata kwarya-kwaryar zanga-zanga don nuna adawa da matakin Taliban na rufe shagunan gyaran gashi da jiki a kasar.
Kungiyar ta haramta wa ‘yan mata zuwa makarantun Sakandire a kasar, sannan ta hana mata karatun jami’a.
An kuma haramta wa mata da ‘yan mata shiga wuraren shakatawa da wuraren motsa jiki tare da hana su aiki a kungiyoyi masu zaman kansu, sannan ta tilasta musu bin tsari wajen sanya tufafi.
A baya Majalisar Dinkin Duniya ta ce mata sun bayar da rahotonnin ” nuna musu wariya, da zalunci da kange su daga samun ‘yancinsu, da tilasta musu zama a wuraren da ke da yanayi irin na gidajen yari”
Da dama daga cikin matan sun bayyana cewa matukar ba su yi aiki ko suka samu tallafi ba, da wuya su iya samun manyan abubuwan bukatunsu na yau da kullum.