A Daren Jiya An Yi Taho Mu Gama A Tsakanin Samarin Palasdinawa Da Jami’an Tsaron HKI A Yammacin Kogin Jordan.
Tashar talabijin din “Palestine Today” ta bayar da labarin cewa; Tun da marecen jiya Lahadi ne dai tahomugamar ya barke a tsakanin samarin Palasdinawan da kuma ‘yan sahayoiya a mashigar garin Ariha dake yammacin kogon Jordan.
“ Yan Sandan haramtacciyar Kasar Isra’ila sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye akan samarin Palasdinawan.
Har ila yau, an yi irin wannan taho mu gama din a cikin garurwa da daman a yankin yammacin kogin Jordan, a matsayin nuna fushin palasdinawa dangane da keta hurumin masallacin Kudus da ‘yan sahayoniyar suke yi.
RAED MORE : Iran Ta Ce; Kona Al’kur’ani Mai Girma Da Aka Yi A Kasar sweeden Cin Zarafin Musulmi Biliyan Daya Ne.
Da asubahin jiya Lahadi ne dai yahudawa 500 su ka yi kutse cikin haraba da farfajiyar masallacin Kudus, bisa kariyar sojojin HKi. A ranar juma’ar da ta gabata ma dai ‘ yan sahayoniyar sun yi wannan irin kutsen a cikin masallacin Kudus mai albarka, lamarin da ya jawo mayar da martani daga al’ummar Palasdinu.
READ MORE : Kasashen Musulmi Sun Yi Tir da Hare-haren Da isra’ila Ta Kai Kan Falasdinawa.
READ MORE : Matsalar Tsaro; Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP.