Aƙalla mutum 200,000 suka yi gudun hijira daga Ukraine zuwa makwabta.
Wasu sabbin alƙalumma sun nuna cewa kimanin mutum 200,000 suka yi gudun hijira daga Ukraine zuwa makwabta.
Hukumomin Slovakia sun ce cikin sa’a 24 daga 6 na safiyar Asabar, kusan mutum 10,000 suka shiga ƙasar daga Ukraine.
Ƴan Ukraine sama da mutum 43,000 suka tsallaka Romania a kwanaki uku da Rasha ta ƙaddamar da mamayar ƙasar, yayin da 150,000 suka shiga Poland.
Ukraine tana kuma iyaka da ƙasashe huɗu – Hungary da Moldova, inda dubban mutane suka tsallaka ƙasashe da kuma wasu da suka shiga Belarus da Rasha.
Shugaban Ukraine ya roƙi ƙasashen duniya su zo su yaƙi Rasha
Shugaban Ukraine ya roƙi mayaƙa na ƙasashen waje da su haɗa ƙawance a Ukraine domin yaƙar Rasha.
Shugaba Zelensky ya yi wannan kiran a shafukansa na na sada zumunta inda ya gayyaci ƙasashe da su goyi bayan Ukraine.
Sanarwar ta ce: “Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky yana kira ga dukan al’ummar duniya, abokan Ukraine, masu son zaman lafiya da ci gaban demokradiyya.
“Duk wanda ke son tsaron Ukraine, Turai da kuma duniya yana iya zuwa ya taimaki ‘yan Ukraine yaƙar masu aikata laifukan yaki na Rasha.”
Shugaban na Ukraine ya sha nanata yadda aka bar ƙasarsa ta kare kanta da kanta