Aƙalla Falasɗinawa 32,705 Isra’ila ta kashe a Gaza a cikin sama da watanni biyar da ta ɗauka tana kai hare-hare a Gaza, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta bayyana.
Aƙalla adadin ya haɗa da mace-mace 82 da aka samu a sa’o’i 24 da suka gabata, inda ma’aikatar ta ce mutum 75,190 aka raunata zuwa yanzu a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba.
Hezbollah ta sanar da kai hari kan sojoji da motocin yaƙin Isra’ila
Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta kai hari kan sojoji da motocin yaƙin Isra’ila a kudancin Lebanon.
Kungiyar ta ce ta kai hari da makami mai linzami kan motocin a yankin al-Malikiyye sai kuma a yankin al-Mitille sun yi amfani da jirgi maras matuƙi na kamikaze domin kai harin, kamar yadda kungiyar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
Haka kuma ta ce ta kai hari kan sojojin na Isra’ila a yankin Hadeb Yarun ta hanyar amfani da makaman atilari.
Hamas da Islamic Jihad sun bayar da sharuɗa huɗu na nasarar yarjejeniyar tsagaita wuta
Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa da ta Islamic Jihad sun bayar da sharuɗɗa huɗu idan har ana so a samu nasara a yarjejeniyar tsagaita wutar da ake shirin yi da Isra’ila.
Daga cikin abinda suke nema har da barin mutanen da suka rasa muhallansu komawa gidajensu da ke Gaza.
Shugaban ɓangaren siyasa na Hamas Ismail Haniyeh da kuma wata tawaga ta ƙarƙashin jagorancin sakataren Islamic Jihad Ziyad al-Nakhalah sun haɗu a Tehran babban birnin Iran.
DUBA NAN: Dalibai Sun Rasa Rayukan Su A Cinkoson Karbar Taimakon Abinci A Jami’ar Nasarawa
A wata sanarwa da Hamas ɗin ta fitar, ta ce domin tabbatar da wannan yarjejeniya ta yi nasara, dole ne a dakatar da hare-haren da ake kaiwa a Gaza, da janye dakarun da ke ƙawanya, da komawar waɗanda suka rasa muhallansu gidajensu da kuma barin kayan agaji shiga.