Kasar Mali, ta bukaci jakadan faransa a kasar da ya tattara nasa ye nasa ya bar kasar cikin kwana uku.
Wannan matakin ya biyo bayan gayyatar da ma’aikatar harkokin faransa ta yi wa jakadan na faransa, Joël Meyer, a ranar Litini inda ta nuna masa bacin ran mahukuntan kasar game da wasu kalamai da ta danganta da na batanci da ministan harkokin wajen faransar Jean Yves Le Drian ya firta kan sojojin dake rike da mulki a kasar.
Shi dai Jean Yves le Drian ya danganta gwamnatin rikon kwaryar ta Mali da haramtaciyya, lamarin da bai yi wa mahukuntan Malin dadi ba.
Hakan ya kara fiddo yadda danganta tsakanin kasashen biyu ke dada tsami, bayan shafe dogon lokaci na cacar baki.
Malin, ta nanata cewa a shirye take wayen tuntubar juna tsakaninta da abokan huldarta na kasa da kasa har da faransa amma cikin mutunci da girmama juna, ba kuma tare da shishigi ba.