Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya ce yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare na shekaru 25 tsakanin Iran da kasar Sin da aka rattabawa hannu a kanta a cikin watan Maris din shekarar da ta gabata, ta fara aiki a wani bangare na sakamakon wata muhimmiyar ziyara da ya kai kasar Sin bisa gayyatar da takwaransa na kasar ta Sin Wang Yi ya yi masa.
Iran da China sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare na tsawon shekaru 25 a watan Maris din shekarar da ta gabata, a wani mataki na kin amincewa da takunkumin da Amurka ta kakaba mata na karfafa kawancen tattalin arziki da siyasa na dogon lokaci.
Yarjejeniyar a hukumance tana kunshe da cikakken tsarin huldar abokantaka tsakanin kasashen Sin da Iran da aka bayyana a yayin ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Iran, don bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu cikin shekaru 25 masu zuwa, da kuma share fagen shigar kasar Iran a cikin aikin samar da ababen more rayuwa wanda ya tashi daga Gabashin Asiya zuwa Turai.
A yayin ganawar, Amir-Abdollahian ya yi ishara da muhimmancin yarjejeniyar hadin gwiwa ta shekaru 25 da aka kulla tsakanin Teheran da Beijing, inda ya jaddada cewa, aiwatar da daftarin zai zama wani muhimmin lamari da kuma wani muhimmin sauyi a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin gaba daya tana goyon bayan matakin da Iran ta dauka na hikima game da manufofin Amurka na cin zarafi, da ma matsayinta kan tattaunawar da ake yi da sauran kasashe biyar da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015, yana mai yin kira ga Washington da ta cika alkawarin da ta dauka.
Wang ya ce, kasar Sin a shirye take ta inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin kudi, makamashi, banki da al’adu, duk da takunkumin da aka kakaba ma Iran ba bisa ka’ida ba.