Ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Iran ta bada sanaran cewa a jiya Asabar ce aka sami mafi karancin adadin wadanda suke kamuwa da cutar Covid 19 a cikin fiye da shekara guda.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata mutane 1,686 suka kamu da cutar a yayinda wasu 58 suka rasa rayukansu, wannan adadin shi nemafi karanci a cikin kwanaki 460 da suka gabata.
Labarin ya kara da cewa a cikin wannan adadin muatne 286 aka kwantar da su a asbiti. Jimikllar mutane 6,152,524 suka kamu da cutar tun farkon shekara ta 2020, sannan 5,963,373 daga cikinsu sun warke. A halin yanzu muatne 3.126 ne kawai suke bangaren kula na musamman a asbitocin kasar. Sannan an yiwa mutane 39,951,481 gwajin cutar.
Read More: Yadda Kafafen Yada Labaran Duniya Suka Bayyana Atisayen Sojin Iran
A Bangaren alluran riga kafin cutar kuma mutane 49,157,835 aka yiwa alluran har sau biyu, sannan 2,237,841 sun sami na uku. Gaba daya an yiwa mutane alluran riga kafin har sauk 109,990,742 a kasar. Wannan ya ya kawo ci gaba da kai ga ba wanda yam utu a jiya a larduna 19 ko kuma mutum daya kacal ya rasu saboda cutar.