Ministan harkokin wajen kasar Iran Husain Amir Abdullahiyan ya bayyana cewa gwamnatin kasar America tana kokarin raba kasar Afganistan da makobtanta saboda wannan yana daga cikin manufofinta a dukkan kasashen yankin.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin America ta mayarwa kasar Afganistan kudadenta da ta rika don gwamnatin kasar ta warware matsalolin tattalin arzikin da mutanen kasar suke fama da su.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abdullahiyan yana fadar haka ne a lokacinda yake ganawa da ministan harkokin waje na riko na gwamnatin Afganistan Molawi Amir Khan wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran.
A nashi bangaren Amir Khan ya yabawa Jumhuriyar Musulunci ta Iran kan daukar bakoncin miliyoyin mutanen kasar Afganistan a cikin shekaru 43 da suka gabata. Ya kuma kara da cewa sabuwar gwamnatin kasar Afgansitan ba zata yi adawa ga wata kasa daga kasashen da suke makobtaka da ita ba.