Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Saeed Khatibzadeh, ta tabbatar da ganawa tsakanin ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian, da takwaransa na Saudiyya, a daura da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, da ya gudana a birnin Islamabad na Pakistan.
- Khatibzadeh, ya sanar a yayin taron manema labarai da ya saba gudanarwa mako mako cewa babu dai wani ci gaba da azo a gani da aka samu tsakanin bangarorin biyu kawo yanz.
‘’Muna har yanzu jiran amsa daga mahukuntan Riyad, a duk lokacin da suka nuna da gaske su ke zamu ci gaba da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi yankin daman a tsakanin juna, inji kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran.
A daya bangaren kuma ya ce suna kira ga Saudiyya, da ta rumgumi hanyoyin diflomatsiyya ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe.