Jami’an tsaron yahudawan sahyoniya sun kai hari kan masu zanga-zangar lumana ta Palasdinawa a unguwar Sheikh Jarrah da ke birnin Quds.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da raoton cewa, sojojin gwamnatin yahudawan Isra’ila sun kai hari kan wani gangamin nuna goyon baya ga al’ummar unguwar Sheikh Jarrah da ke birnin Kudus a ranar jiya Juma’a 17 ga watan Disamba.
Jama’a da dama ne suka taru a unguwar bayan sallar Juma’a, domin nuna goyon bayansu ga al’ummar wannan unguwa ta Sheikh Jarrah, musamman iyalan Salem, wadanda kotun Isra’ila ta kwashe su daga yankin kwanakin baya.
A shekarar da ta gabata ne wata kotun yahudawa a birnin Quds ta yanke hukuncin korar mazauna yankunan Falasdinawa 12 da ke unguwar Sheikh Jarrah.
Hukuncin ya tilasta wa iyalai hudu barin gidajensu a watan jiya. Sai dai sun yi amfani da ‘yancinsu na yin zanga-zanga da daukaka kara, kuma aka ci gaba da shari’a kan batun.
A ranar 3 ga watan Janairu, gwamnatin Isra’ila ta aike da sanarwa ga iyalai hudu na Falasdinawa da su bar gidajensu, bisa da’awar cewa filayen da aka gina wadannan gidaje na Yahudawa ne tsawon shekaru da dama.
A shekarar da ta gabata Isra’ila ta kwace wasu gidajen Falasdinawa da ke unguwar Sheikh Jarrah, da nufin mika su ga yahudawa masu yin hijira daga kasashen duniya zuwa Isra’ila.