Jakadan kasar Iran a MDD ya ce an mayarwa kasarsa hakkinta na kada kuri’a a majalisar bayan da aka dakatar da shi na ‘yan kwanaki saboda rashin biyan kudaden karo-karo wadanda ko wace kasa take biyan majalisar a ko wacce shekara.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Majid Takht Ravanchi jakadan kasar Iran a MDD yana fadar haka a jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa, kasar Korea ta Kudu ce ta biya kudaden a madadin jamhuriyar musulunci ta Iran, bayan da ta hana kasar taba kudadenta kimanin dalar Amurka biliyan 18 wadanda suke cikin bankunan kasar saboda biyayya ga Amurka na hana Iran taba kudadenta.
Shekaru biyu kenan a jere ake hana kasar Iran hakkinta na kada kuri’a a majalisar dinkin duniya saboda rashin biyan kudaden da yakamata ta biya majalisar a cikin lokaci. Kafin haka dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sa’eed Khadib Zadeh ya yi kira ga babban sakataren MDD Antonio Guterres da dubi kasashen da aka dorawa takunkuman zalunci a duniya ya kuma dauki matsayi na musamman a kansu don irin wahalar da suke sha saboda wadannan takunkuman.