Shugaban muhammadu Buhari wanda ya kai ziyarar aiki a jihar kaduna a makon da ya gabata, ya bayyana cewa sojojin kasar tare da sauran jami’an tsaro suna yin kokarin da zasu iya yi don ganin bayan yan ta’adda a arewacin kasar.
Jaridar Premium times ta nakalto Shehu Garba mai bawa shugaban shawara kan al-amuran watsa labarai yana fadar haka, ya kuma nakalto shugaban yana fadar haka a gidan gwamnati na jihar Kaduna, inda ya kara da cewa ya san irin mummunan halin da matsalolin tsaro a jihar da kuma sauran jihohin arewacin kasar suke ciki, amma ya kara jadda cewa gwamnatinsa tana matukar kokarinta na ganin an ga bayan wannan matsalar kafin wa’adin mulkinsa ya ciki a shekara mai zuwa.
Shugaban ya bude sabbin manya-manyan ayyuka ci gaba a jihar ta Kaduna wadanda gwamnatin Ahmed El-Rufa’ee ta gina. Ayyukan dai sun hada da filin wasanni da Ahmadul Bello dake Kaduna, sabon kasuwar sabon gari gadar Kawo da sauransu duk a jihar ta kaduna.