Labaran da suke fitowa daga fadar shugaban kasa a tarayyar Najeriya sun bayyana cewa wasu makusanta ga shugaban kasa sun kamu da cutar Covid 19.
Jaridar Premium times ta najeriya ta bayyana cewa an bayyana sakamakon gwajin da aka yiwa wasu daga cikin makusantan shugaban kasar ne a karshen makon nan.
Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda abin ya shafa dai, har da kakakin fadar shugaban kasa kuma babban mai bashi shawara kan al-amuran watsa labarai wato Malam Shehu Garba.
Kafin haka shehu Garba ya tabbatar da haka ta wani sakon rubun da ya watsa cikin shafinsa na sadarwa. Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da Tijjani Umar babban sakare a fadar shugaban kasa, Yusuf Dodo mai taimakawa shugaban kasa a kan wasu al-amura na musamman.
Daga cikin ministoci kuma akwai Alhaji Lai Muhammad ministan watsa labarai, da Aliyu Musa, wato dogarin shugaban kasa.
Shehu Garba ya bayyana cewa bai sanda labarin sauran wadanda suka kamu da cutar ba banda shi, amma ya tabbatar da cewa ya yi alluran riga kafin cutar har guda ukku kafin hakan ya faru. Mai yuwa shi yasa cutar bata yi masa tsanani ba, amma tuni ya sami sauki harma yana motsa jiki a jiya Asabar bayan killacewa da yakewa kansa da kuma fara shan magani.