Ƴan sanda sun sake rufe Majalisar Dokokin Jihar Plateau
Ƴan sanda sun sake rufe majalisar dokokin Plateau, a Jos babban birnin jihar da ke arewa maso tsakiyar Najeriya lamarin da ya haifar da zaman zullumi da neman tayar da hakarkari a harabar a yau Laraba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani dan majalisar, Gwottson Fom daga mazabar Jos ta Kudu ya tabbatar mata da haka.
Dan majalisar wanda ya soki abin da ƴan sandan suka yi, ya ce matakin ya hana mambobin zamansu na yau Laraba.
Ya ce, ”mun yi zamanmu jiya (Talata) ba tare da wata matsala ba, kuma mun duba wasu kudurorin doka masu muhimmanci tare da zartar da wasu kudurori domin amfanin mutanenmu.
Mun shirya sake zama yau (Laraba) mu ci gaba da aikinmu na majalisa amma sai kawai ƴan sanda suka zo suka rufe majalisar.
Ya kara da cewa a matsayinsu na ƴan majalisa ba su san abin da zai sa ƴan sanda za su zo su rufe musu majalisa ba su hana su aiki.
”Za mu yi taron manema labarai mu gaya wa duniya abin da ke faruwa a jihar Palteau saboda ƴan sanda na neman kashe dumukuradiyya a Plateau,” in ji shi.
Tun wata biyu da ya gabata ƴan sanda suka rufe majalisar a bisa abin da suka ce umarni daga hukumominsu kuma tun lokacin suka kasa suka tsare a harabar, lamarin da ya hana mambobin zama.
sai shekaran jiya Talata, kusan sa’a 24 bayan rantsar da sabn gwamnan jihar Caleb Mutfwang, wanda ya gaji Simon Lalong.
Yanu dai an danda sun ce sun sake rufe majalisar ne domin hana tabarbarewar rikicin da ake yi a kan shugabancin majalisar.