Ƴan bindiga sun kashe sojojin Nijar shida.
An kashe sojojin Nijar shidaa wani hari da ƴan bindiga suka kaia kudu maso yammacin ƙasar, kusa da iyaka da Burkina Faso, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar ranar Asabar.
Harin wanda aka kai a ranar Alhamis, shi ne na biyu cikin kwanaki 10 da ke nuna dawowar hare-hare a yankin bayan shafe makwanni ba a kai hari ba.
Sanarwar ma’aikatar tsaron ta ce “Wasu gungun ƴan ta’adda ɗauke da makamai sun yi wa ayarin sojojin Nijar kwanton ɓauna a kusa da kauyen Kolmane.”
READ MORE : Ɗan majalisar Amurka ya rasa kujerarsa saboda ɗan Najeriya .
Sanarwar ta ce sojoji shiga aka kashe yayin da ɗaya ya samu rauni da kuma mota da aka lalata. Babu ƙarin bayani kan makomar maharan.
Yankin Tallaberi ya sha fama da hare-hare musamman a yankunan da ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali inda mayaƙa masu iƙirarin jihadi masu alaƙa da Al Qaeda da IS ke kai hare-hare.