Dan shugaban kasa Bola Tinubu, Seyi Tinubu ya bayar da gudummawar Naira miliyan 500 ga wadanda ambaliyar ruwa ta Maiduguri ta shafa.
Ambaliyar ruwa da ta addabi jihar Borno a makon da ya gabata ta lalata kashi 70 cikin 100 na birnin tare da raba miliyoyin mazauna garin.
Dan Shugaban kasar wanda ya samu rakiyar dan uwansa, da abokansa ya ce sun je Maiduguri ne domin jajanta wa wadanda abin ya shafa.
Da yake jawabi Gwamna Babagana Zulum da sauran manyan baki da suka tarbe shi a gidan gwamnatin jihar, Seyi ya yabawa yadda ‘yan kasar suka jajirce duk da rashin tsaro da ya addabi jihar a shekarun baya.
Ya ce, “Muna nan a yau, ba wai a matsayinmu na ‘yan gidanmu kadai ba, a’a a matsayinmu na ’yan kungiyar hadin kan matasan Najeriya don samar da fata da walwala ga wadanda suka fi bukatar hakan. Wannan lokaci ne na haɗin kai, tausayi, da kuma ɗaukar matakai na gaggawa.
“Maiduguri a jihar Borno tana da dimbin tarihi. Mutanen suna da juriya. Duk da al’amuran da suka faru a shekarun baya, sun jajirce wajen ganin an shawo kan lamarin, wanda hakan ne ya sa irin wannan bala’i mai radadi na kasa da ya addabi jihar, ya dace mu hada kai, goyon baya da addu’a. Har ma fiye da haka, ya cancanci haɗin gwiwa da gudummawarmu.
“Lokacin da mahaifina, Shugaba Bola Tinubu, ya ziyarci Maiduguri a farkon makon nan, ya yi magana game da bukatar kamfanoni masu zaman kansu da kuma daidaikun mutane su tashi tsaye don tallafawa al’ummomin da abin ya shafa. Ta hanyar kiransa, ni da matata Layal, ta hanyar gidauniyar Noella, da dan uwana Yinka, abokanmu, da sauran kamfanoni masu zaman kansu, mun hada hannu don amsa gaggawar bukatun wadanda suka rasa muhallansu sakamakon wannan bala’i.”
Haka kuma an bayar da tallafin ga jihar har guda 10,000 na gidajen sauro, barguna, katifu, tankuna, nannade, bokiti, tabarmi, kayan tsafta da kayan wanke-wanke.
Da yake mayar da martani, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yabawa Seyi da tawagarsa, inda ya yi alkawarin cewa za a yi amfani da tallafin da aka ba su domin cimma burinsu.
Duba nan:
- Najeriya da zabin kasar China _ Zainab Suleiman Okino
- Zulum hails Seyi Tinubu over N500m donation to flood victims