Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce fatara da talauci na iya tilastawa wasu da ke sansanin yan gudun hijira shiga kungiyoyin ta’addanci.
Zulum ya yi wannan jawabin ne a jiya Alhamis yayin da ya ke jawabi wurin taron rufe wasu sansanonin yan gudun hijira a jihar Borno yana mai cewa ya zama dole a taimakawa mutane su koma gidajensu su fara sana’a.
Gwamnan na Borno, ya yi alkawarin cewa kafin wa’adin gwamnatinsa ta kare za a rufe dukkan sansanonin ya kuma ce dole gwamnati ta magance ainihin dalilin da ya haifar da matsalar don samun zaman lafiya mai dorewa.
Gwamna Jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana fargaba kan karancin kudi da fatara, idan ba a magance shi ba, na iya tilasta wasu mutanen da ke sansanin gudun hijira shiga Boko Haram ko ISWAP, rahoton Daily Trust.
Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a jiya yayin rufe sansanin yan gudun hijira na Dalori-1, Dalori-2 Gubio da Muna a Maiduguri, ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da ajiye mutanenta a sansanin yan gudun hijirar ba.
Zulum ya ce: “Hanya guda da za a magance matsalar yan ta’adda shine gwamnati ta magance sillar abin wanda ya hada da karuwar talauci, rashin ababen cigaba da matsalar dumamar yanayi.
“Don haka, abin da ya kamata mu yi shine mayar da yan gudun hijira gidajensu cikin mutunci, Ba a tilasta wa kowa komawa gidansa ba, muna farin cikin tallafa musu komawa gidajensu bisa tsarin taron Kampala.
Za a tallafawa mutane da sana’a don su cigaba da rayuwarsu idan ba haka ba mutanen mu za su cigaba da zama a sansanin yan gudun hijira,” in ji shi.
Source:hausalegitnghttps