Gwamnan Jihar Borno dake Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana dalilan da zasu hana shi karbar tayin zama mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Yayin da yake tsokaci wajen zaben fidda gwanin da Jam’iyar APC ta gudanar yau a Maiduguri wanda ya tabbatar masa da tikitin takarar yin wa’adi na biyu, Zulum yace ya karbi sakonni daban daban daga wasu na kusa da masu neman tikitin takarar shugaban kasa domin mara musu baya a zaben mai zuwa.
Zulum yace bayan zulumi da nazarin da yayi akai da kuma kimar dake tattare da kujerar mataimakin shugaban kasar, musamman jagorancin taron majalisar tattalin arziki da damar amfani da jiragen saman fadar shugaban kasa da kuma yadda ake tarbar mai rike da ofishin a kasashen duniya da kuma makomar jama’ar sa ta jihar Borno da ayyukan da ya sa a gaba, ya yanke hukuncin kin karbar tayin.
Gwamnan yace ya tambayi kansa idan ya karbi kujerar mataimakin shugaban kasar wadda zata daga darajar sa a siyasance me zai zama makomar dinbim ayyukan jama’ar da ya sa a gaba?
Zulum yace gwamnatin sa ta gina gidaje sama da 10,000, yayin da take ci gaba da gina wasu kari yanzu haka domin tsugunar da wadanda suka rasa gidajen su, bayan mayar da al’ummomi sama da 20 garuruwan su.
Gwamnan yace tabbas har yanzu akwai dubban mutanen da basu da gidaje kuma suna bukatar agajin abinci da ruwan sha da kuma kula da lafiyar su, kuma gwamnatin sa ta tsara shirin da zai bata damar tinkarar matsalar.
Zulum yace kisan gillar da aka yiwa jama’a a Kala-Balge a karshen mako ya jefa masa tunani mai zurfi akan kalubalen dake gaban su a Jihar Borno, saboda haka ya yanke hukuncin ci gaba da zama a Borno domin yiwa jama’ar sa aiki.
Gwamnan wanda ya godewa yan siyasa daga matakai daban daban da suka neme shi domin tsayawa takarar mataimakin shugaban kasar, ya basu hakuri wajen ganin sun taimaka masa ci gaba da gudanar da aikin sa a Jihar Barno domin sauke nauyin da ya rataya akan sa.