Labarai daga majiyoyi masu tushe daga birnin zariya na tabbatar da cewa, jami’an tsaron Najeriya cikin kayan aiki sun aukawa wasu dandazon fararen hula masu gangamin nuna bakin ciki da zagayowar ranar raauwar Sayyidi Husaini jikan Manzon Allah (S.a.w.w).
Masu juyayin wadanda aka tabbatar da cewa akasarin su almajiran Malam Zakzaky ne suna tafiya cikin tsari gami da lumana kamar yadda suka saba duk shekara amma sun gamu da harbe harben jami’an tsaro wadanda ba tare da jiran komi ba suka auka musu da harbi tare da amfani da harsashi mai rai a kan fararen hulan.
Tun da farko rahotanni sun tabbatar da cewa, a dai dai unguwar baban dodo dake zariya jami’an tsaro suka tari masu makokin na Sayyidina HUSAINI kuma tun a lokacin masu juyayin sun bukaci dalilin hakan amma maimakon samun amsa sai ruwan harsasai suka samu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe wani mai suna Muhammad Hamisu Dan unguwar yakasai kuma da dama sun tsira da raunuka manya da kanana.
Mabiya Malam Zakzaky dai sun saba fitowa irin wadannan taruka duk shekara fiye da shekaru arba’in kuma a lokuta da dama a kan samu jami’an tsaro su afka musu ba tare da wani dalili ba.
Ranar goma ga watan muharram dai itace ranar da aka kashe jikan Manzon Allah (s.a.w.w) a wata sahara dake kasar Iraqi wacce ake kira da karbala.
Tarihi ya tabbatar da cewa tun wancan lokaci mabiya ahlulbayty wadanda aka Fi sani da ‘yan shi’a suka mayar da wannan rana ta makoki domin nuna bakin cikin su da wannan lamari da ya faru wanda alkaluman tarihi suka rubuta.
Zuwa yanzu mabiyar mu bata samu tattaunawa da bangaren jami’an tsaro ko ofishin Malam Zakzaky ba, sai dai majiyoyi sun tabbatar mana da cewa mabiya Malam Zakzaky din sun dauki gawar wanda aka harbe kuma basu dauki wani matakin da ya saba doka ba.