An bude taron karawa juna sani kan bukasa kimiyyar karatu daga nesa a babban dakin taro na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (Assembly hall).
Manyan mutane sun gabatar da mukaloli da dama da suke kira akan bunkasa harkar kimiyyar karatu daga nesa tare da kawo amfaninsa ga al’ummar kasa da kuma magance kalubalen da ke cikinsa.
Daga cikin manyan bakin da suka sami halartar wannan taro akwai wakilin babban sakataren Hukumar Kula da Jami’o’I ta Kasa, Mista Chris J. Mai Yaki, da wakilin Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Farfesa Ahmed Dako Ibrahim da Hajiya Rakiya Gambo Iliyasu, darakta daga U.E.F da sauran manyan baki daga kasashen ketare
Bayan kammala bude taron ne, shugaban kwamitin taron kuma shugan tsangayar karatu daga nesa (Distance Learning) na Ahmad Bello Zaria Farfesa Ibrahim Sule ya yi wa manema labarai karin haske kamar taron wanda ya bayyana cewa idan ‘Yan Nijeriya suka rungumi tsarin, za a samu karin mutane da suka halarci manyan makarantu a Nijeriya.
A wani labarin na daban cibiyar kula da hada maguna ta Nijeriya tare da hadin gwiwar hukumar kula da ilimin da fasaha sun bayar da horo kan fasahar hada maguna a kwalejojin fasaha da kimiyya da ke fadin Nijeriya.
Bayar da horon ya gudana ne a shalkwatan ma’aikatan ilimi, a wani yukuri na hada kan masu ruwa da tsaki kan fasahar hada maguna.
Karamin ministan ilimi, Dakta Tanko Sununu shi ya jagoranci taron bayar da horon,wanda ya samu halartar sakataren ma’aikatar ilimi da sauran daraktoci.
Dukkan bangarorin guda biyu wadanda suka dauki nauyin bayar da horon sun amince a bai wa daliban da ke karatun difiloma ne kadai. Sun yaba wa shugabannin ma’aikatar ilimi wajen kokarin karfafa musu gwiwa kan bayar da wannan horo na fasahar hada maguna.
DUBA NAN: Zulum Ya Amince Da Fitar Da Kudi Domin Tallafawa Ɗalibai
Sun kara da cewa a cikin nasarorin da aka cimma sun yi daidai da manufofin wannan gwamnati ta Shugaban kasa, Bola Tinubu na kara inganta harkokin kiyon lafiya.