Al’ummar Unguwar Mangwaron Agwai da Malalin Gabas da ke cikin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, sun fada cikin rudani kan bayyanar wata mata da suke zargin mayya ce.
Al’ummar wadanda tuni suka fara tserawa suna barin gidajensu domin neman mafaka a unguwanni makwabta.
lamarin ya faru ne ranar litinin 11 ga watan Satumbar 2023 da misalin karfe 2 na rana, ganin yadda matan suka fito tsirara babu kaya a jikinsu suna yawo layi-layi suna sumbatu lamarin da haifar da tsoro da fargaba a unguwar, musamma mata da matasa.
Ganin Hakan ya sanya wasu fusatattu suka kama wata mata mai shekaru kusan 55 suka lakada mata dukan kawo wuka, wacce da kyar jami’an tsaron sai kai na JTF suka kwace ta.
Da farko dai matar ta tsorata kowa hatta jami’an tsaron na JTF sun fara gudu daga ofishin nasu sai daga bisani da suka fahimci cewa matar kamar tana da tabin hankali, hasalima, idan suka bar matasa da matar suna iya daukar doka a hannunsu na yin kisa.
Lokacin da wakilinmu ya shiga unguwar ya yi kicibis da mata da yara suna gudu suna addu’oin neman kariya daga Allah, lamarin da ya kai matan aure suna ta rufe gidanjensu suna barin gida. Wasu mata da wakilinmu ya ci karo da su ya ga suna gudu suna kiran ” mun shiga uku mayu sun shigo mana gari! Ga su can mayu ne su biyu !! .
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa matar tana fama da tabin hankali ne ba maita ba, musamman ganin yadda ‘Yan JTF suka rinka yi wa matar tambayoyi.
A zantawarsa da wakilinmu Sakataren JTF na gundumar Mangwaron Agwai Mohammed Suleiman, ya ce “wasu matasa ne suka lakada wa matar duka bisa zargin ita mayya ce saboda sun ganta tana yawo tsirara babu kaya a jikinta hakan ya sanya mu kuma muka kwace ta a hannunsu”
Ya bayyana cewa “Mun fara samun bayanin ne tun da safiyar litinin din nan cewa wasu mata da ake zargin mayu ne sun bayyana a unguwar Mangwaron Agwai sai muka fara bincike a kai zuwa da rana kamar karfe 2, sai muka ga mutane suna ta guje-guje wai mayu sun bayyana a a unguwarmu kamun kace kwabo har wasu fusatattun matasa sun kama wata mata sun lakada mata duka, sun yi mata jina-jina, nan da nan muka kwaci matar domin yi mata tambayoyi da gudanar da bincike akan lamarin”
Ya kara da cewa ” Bayan mun kammala bincikenmu akanta sai muka fahimci cewa matar tana da tabin hankali wanda tuni muka mikata wurin ‘Yansanda a Rafin Guza, inda nan ma suka tabbatar mana da cewa matar tana da tabin hankali kuma zuwa gobe akwai yiwuwar su sake ta” inji shi.
Unguwar Mangwaron Agwai da Malalin Gabas sun yi kaurin suna wajen samun yawaitar mayu da matsalar rashin tsaro, hakan ya sanya matan aure da yara kanana suke zaman dar-dar a yankin.
Source: LEADERSHIPHAUSA