Akan sayar wa da ’yan acaban tikitin na N50 a kullum a matsayin hanyar karbar haraji, yayin da wadanda suka ki biya akan kwace baburan su, ‘yan achaban sun gudanar da zanga zangar.
Yayin zanga-zangar, ’yan acabar sun fasa tagar sakatariyar kungiyarsu, kafin su wuce zuwa fadar Sarkin Gombe domin mika kokensu.
Daya daga cikin masu zanga-zangar mai suna Abdullahi Bongos ya ce, “An daki wani dan acaba har sai da ya fadi a kasa. Sun zaci ko da wasa yake da ya kwanta bayan dukan nasa, har sai da aka kai shi asibiti kafin a gane munin yanayin da yake ciki
“Lamarin ya faru ne a kusa da tashar motar Gombe. Mun ji labarin ya rasu ’yan sa’o’i bayan an kai shi asibiti.
“Yanzu kuma wai suna ce mana an sallameshi ba tare da sun bari mun ganshi ba. Da ’yan sanda da shugabannin kungiyarmu na yi mana rufa-rufa ne kawai,” inji Abdullahi.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar, SP Mary Malum, ta karyata labarin cewa dan acabar ya rasu ne jim kadan da kai shi asibiti.
A cewarta, tuni aka umarci masu aikin sayar da tikitin da su dakatar da aiki har sai an yi taro ranar Talata mai zuwa
“Ina sane da labarin zanga-zangar, amma dan acabar bai mutu ba. Wakilan kungiyarsu za su gana da Shugaban Karamar Hukumar Gombe ranar Talata, su kuma masu aikin sayar da tikiti a hanyar an umarcesu su dakatar har sai Talata,” inji Maryam.
Ba a gombe kadai ba a fadin najeriya ma gabadaya ana iya cewa al’umma suna cikin halin matsi da neman taimako saboda haka babu bukatar kara musu zafi ta hanyar sanyawa masu kananan sana’o’i haraji.