A yau ranar Talata, 26 ga watan Yulin 2022, Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta fito kwanta da kwartata a titunan jihohin kasar nan domin zanga-zangar kara ga Kungiyar.
Malamai masu koyarwa na jami’o’in Najeriya ASUU.
Malaman jami’o’in Najeriya sun shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kuma har yanzu babu ranar karshenta.
Legit za ta kawo muku bayanai kai tsaye kan yadda zanga-zangar ke gudana. 12:16 Yamma Bidiyo: Kungiyar Kwadago ta Jigawa da ta dalibai sun shiga zanga-zangar taya ASUU nuna fushi.
Mambobin kungiyar kwadago reshen jihar Jigawa sun bi sahun takwarorinsu na sauran jihohi wajen shiga yajin zanga-zangar lumana don nuna goyon bayansu ga kungiyar malaman ASUU.
Hakazalika, shugabannin kungiyar dalibai da kungiyoyin fararen hula a jihar sun bi sahunsu inda suka yi tattaki a garin Dutse, babbar birnin jihar ta Jigawa. 11:11 Safiya.
Kungiyar Kwadago ta Osun ya fito kwai da kwarkwata domin shiga zanga-zangar taya ASUU nuna fushi.
Mambobin kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Ogun sun fito zanga-zangar lumana a Abeokuta domin nuna goyon bayansu ga kungiyar malaman jami’o’i.
Members of the NLC Jigawa, student Union leaders & civil society organizations join ASUU to protest the closure of Nigerian universities in the capital, Dutse.#SSANU #NASU #ASUU #NLCProtest pic.twitter.com/9itwwq976M
— Channels Television (@channelstv) July 26, 2022
Jihohi da yawa ne suka shiga wannan zangaa-zangar hadin gwiwa da kungiyar malaman jami’o’i da ke yajin aiki watanni sama da hudu. 11:05 Safiya.
Kungiyar Kwadago a Gombe ta shiga sahu a zanga-zangar lumana ta hain gwiwa da ASUU Wani bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta ya nuna lokacin da mambobin kungiyar NLC suka fito kwai da kwarkwata domin taya ASUU zangaa-zangar lumana a birnin Gombe ta Arewa maso Gabas. 10:56 Safiya.
Ma’aikata sun taru a gaban ofishin NLC a Port Harcourt Ma’aikata suna taruwa a kan titin Igboukwu, D-Line, Port Harcourt, kusa da ofishin kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC da a yanzu yan sandan Najeriya suke rufe.
Source:hausalegitng